Yadda ake yiwa Fasahar AI (Artificial Intelligence) tambaya Domin samun sakamo mai Kyau
Kusan kowa yanzu yana yin amfani da Æ™irÆ™irarriyar Fasahar AI (Artificial Intelligence) wajen sauÆ™aÆ™a al’amuransa da suka shafi aiki, sana’a kasuwanci da harkokin yau da kullum. Amma mafi yawa daga cikin mutane basu san hanyoyin da zasu bi domin suyiwa manhajojin fasahar AI (Generative AI tools) tamabaya wacce zata basu irin sakomakon da suke buÆ™ata. A wannan rubutun zamu kawo muku bayanai akan irin tambayoyin da yakamata kuke yiwa manhajojin fasahar AI (Generative AI tools) irinsu ChatGPT domin samun sakamakon da kuke da buÆ™ata.
Yanda ake yiwa fasahar AI tambaya
Gabatar da Kai:
Idan mutum yanaso fasahar AI tabashi amsa daidai da matakinsa da kuma matsayin ƙwarewarsa akan abinda yake da buƙata AI tabashi amsa akai dole ne yayiwa wannan manhajar AI ɗin bayani game da kansa a taikaice, ya faɗawa AI shi wanene sannan wanne irin matakin ƙwarewa yake dashi.
Misali:
Mutum zaice ni malamin makarantane da yake koyar da dalibai darasin kasuwanci, ya’n matakin aji na biyu a jami’a. Wannan zai sa AI tabawa mutum bayani dadai da abun da ya ke da buÆ™ata.
Bayani akan tambayar da mutum zaiyi:
Yana da kyau mutum yayiwa fasahar AI taƙaitaccen bayani akan wannan tambayar da yayiwa fasahar Ai ɗin, kamar ya faɗawa fasahar AI abun da zayyi da amsar da aka bashi, inda zayyi amfani da wannan bayani, suwaye mutanen da zasu amfana da wannan bayanin da dai sauran bayanai amma a taiƙaice.
Misali: Zankoyar da É—alibai yan jami’a yan aji biyu, darasi akan kasuwancin yanar gizo
Irin Yanda mutum yake so amsarsa ta kasance:
Idan mutum zai tamabayi fasahar AI akan wani abu yana dakyau ya faÉ—awa AI ga yanayin yanda yakeso amsar da za a bashi ta kasance kaman yawan kalmomin (number of words), yawan fejika, adadin sakin layi da kuma irin zurfin bayanin da mutum yakeso AI tayi masa akan wannan tambayar da yayiwa fasahar AI
Misali: mutum yacewa AI inaso amsata kada ta wuce kalma dubu É—aya 1000 sannan inaso bayanina ya kasance yanada sakin layi (paragraph) guda biyu sannan kowanne yayi bayani akan abu kaza da abu kaza
Bayarda Misalai:
Idan mutum zai tambayi AI yana da kyau ya faÉ—awa AI cewa abayanin da zai bashi ya haÉ—a da misalai acikin wannan bayaninn.
Manhajar da mutum zayyi amfani da wannan bayanin da ya samu daga AI:
Yanda kayau mutum ya faÉ—awa fasahar AI cewa zayyi amfani da wannan bayanin da AI ya bashi a manhajoji kaza da kaza, wannan zaisa AI ya bashi bayanin da ya dace da waÉ—annan manhajojin.
Misali: zanyi amfani da wannan bayanan a manhajojin Facebook, X da kuma LinkedIn
MISALI
“Barka dai chatGP ni malamin jami’ane ina koyarda É—aliban jami’a na matakin aji biyu darasin kasuwancin yanar gizo. Ina so ka rubutamin script na bidiyo akan yanda ake kasuwanci a manhajar Facebook, wannan bidiyon kar ya wuce minti biyu sannan zanÉ—ora wannan bidiyon manhajojin Tiktok,Facebook reels da kuma youtube shot,. Zanso ka haÉ—a min da misalai da kuma hanyoyin da zansamu masu kallo da yawa”
A Æ™arshe duk wanda yakeso ya samu sakamakon da ya dace da tambayar da yayiwa fasahar AI wajibine yayi magana da fasahar AI a salon maganar da yakeyiwa É—an’uwnasa Mutum saboda ya baka amsa irin wacce mutum zai baka.
0 Comments