Nemowa Tsofaffin saƙonni (Search Your Chat History)
Wani lokacin mutum zai bukaci wani saƙo da aka turamasa a tsawon lokaci da ya shuɗe saboda wani amfani nashi na karan kansa amma sai ya kasance ya manta wanda ya turamasa saƙon ko kuma dawa sukayi wannan maganar.
Matukar mutum zai iya tuna wasu kalmomi dasu ke cikin wannan saƙon to zai iya nemowa wannan saƙon cikin sauki.
Yanda mutum ze yi (Steps)
Mutum ya buÉ—e whatsapp dinsa >>
Se yaje wajen search (search Icon)>>>
Se mutum ya rubuta kalmomin da zai iya tunawa game da wannan saƙon >>>>
Wannan saƙon ze fito.
Tura saƙonnin da zasu ke ɓacewa alokacin da mutum yakeso ( Send Disappearing Messages):
Whatsapp yana bawa mutum dama ya seta tsarin maganarsa da mutane ta yanda ze iya sawa saƙon da ya turawa mutum ya bace a lokacin da yakeso batare da ya gogeshi ba.
Yanda mutum ze saka (steps)
Ida mutum ya bude Whatsapp dinsa >>
Se ya danna sunan mutumin da yakeso ya sawa (disapearing message)
Se ya danne sunan wanda yakeso ya sakawa
Sai ya danna wajen da aka saka (dsappearing message)
Sai ya zaɓi tsawon lokacin da saƙon zai kasance (awa 24, kwana 7, kwana 90)
Ko kuma
Mutum ze iya zuwa settings
Se ya shiga privacy
Se ya danna default message Timmer
Seya zaɓi lokaci
Lura da ma’ajiyar bayanai (Tracking data storage usage)
Lura da adadin wajen da manhajar whatsapp ta mamaye acikin ma’ajiyar bayanan wayarka yana da matuÆ™ar amfani domin ze taimaka wajen rage cunkoson bayanai daga cikin wayar.
Yanda mutum zeyi (Steps)
Mutum ze shiga setting na whatsapp É—insa
Se ya danna (storage and data)
Se ya danna (Manage storage)
Se ya danna (View usage)
Tura saƙo a whatsapp ta hanyar amfani da Google Assistant
Idan mutum yana amfani da google Assistant a wayarsa, ze iya amfani da google Assistance ɗin kai tsaye ya tura saƙo zuwa ga duk wanda yake so ya turawa a whatsapp batare da ya buɗe manhajar whatsapp akan wayar sa ba.
Yanda mutum zeyi (steps)
Mutum ya buÉ—e google assistance sai mutum yayi magana dashi kaman yace “hi”
Sai mutum ya bashi umarni ya tura saƙo ga wane ya ambaci wanda yake so a turawa saƙon
Manhajoji (Aplplications)zasu fito se ya zaɓi whatsapp
Se ya faɗi saƙon da yake so a tura
Kai tsaye google Assistance ze tura wannan saƙon cikin ƙanƙanin lokaci
Kashe alamar da take nuna mutum ya karanta saƙo
A manhajar whatsapp idan mutum ya tura saƙo akwai alamar da take nuna cewa mutum ya duba wannan sakon ko kuma bai duba ba.
Idan mutum baya buƙatar mutane suke gane cewa ya karanta saƙonsu ko kuma be karantaba ga hanyoyin da za bi ya rufe
Yanda mutum Zeyi (Steps)
Mutum ze shiga settings a whatsapp É—insa
Se ya danna Account and Privacy
Se mutum ya danna read recipient off a WhatsApp
Mayarwa da mutum ɗaya saƙo a cikin group
Idan wani yayi magana a cikin gidan haÉ—aka (group) a cikin manhajar WhatsApp kuma kanaso kamayar masa da magana amma shi kaÉ—ai kakeso ya gani ga yanda zakayi
Yanda mutum zeyi (steps)
Idan kaje kan saƙon se ka danne kan saƙon
Se mutum ya danna É—igonguna dasuke a hannunsa na dama a cikin WhatsApp
Se mutum ya danna reply privately
Karanta saƙon Whatsapp batare da an bude Whatsapp ba
Idan mutum yanaso yake karanta saƙonni da aka turo masa daga whatsapp koda kuwa be buɗe manhajar whatsapp ɗin ba to ga yanda zeyi
Yanda mutum zeyi (Steps)
Mutum ya buÉ—e Whatsapp se ya shiga settings
sannan ya shiga notification
Sai ka sawa “high priority notification” on
Tsayarda saƙonni masu muhimmaci (Pin whatsapp message)
Idan akwai mutanen da mutum yake yawan yin mu’amala dasu musamman ta kasuwanci ko kuma ya’n uwantaka kuma wani lokacin yana shan wahala wajen nemosu idan ze tura musu saÆ™o to bari na koya muku wata dabara da zaku magance wannan matsalar
Yanda mutum zeyi (steps)
Kai tsaye mutum yaje kan sunan mutumin da yake yawan turawa saƙo
Se mutum ya danne kan sunan
Ze ga wasu abubuwa sun fito guda huÉ—u
Ze ga ansaka pin sai ya danna shiikenan
Wannan sunan ze ke tsayawa kullum daga sama.
Tura saƙon bayanin inda mutum yake (location sharing)
Mutum ze iya samun kansa a halin tafiya kuma yanaso ake bibiyar sa saboda wani dalili, ze iya turawa wani ko wasu mutane saƙon inda yake kuma ya basu damar da zasuke bibiyarsa duk inda ya shiga
Yanda mutu zeyi (steps)
Mutum ya buɗe kaman ze tura wa wani saƙo
Se ya danna alamun attached
Ze ga ansaka location
Se mutum ya danna share location sanna se ya seta yau she yake so a dena bibiyayrsa
Wannan yana da matukar amfani musamman saboda yanayi na tsaro.
Yanda ake yin rubutun Italics (I) Bold (B) ko kuma underline a Whatsapp to ga yanda mutum zeyi
Kwanceccen rubutu (Italics I) mutum zee kusa da rubutun sai ya saka wannan alamar (_ ) kai tsaye rubutun zai kwanta
Saka rubutu yayi baƙi sosai (Bold B) agaba da bayan rubutun se mutum ya danna wannnan alamar ((*)
Layika biyu a tsakiyar rubutu a gaba da bayan rubutun mutu ze danna wannan alamar ()
0 Comments