Artificial Intelligence (AI) ko kuma kirkirarriyar fasaha a harshen Hausa ilimin kimiyane da yafi kowanne ilimi saurin yaduwa a duniyar wannan zamani kuma shine fasaha mafi karbuwa a duniyar kimiya da fasaha. Kirkirarriyar  Fasahar (AI) tazo ne domin ta canza taswirar tsarin kimiya da fasaha ta hanyar kwaikwayo da kuma kokarin aiwatar da  fasahar dan Adam a jikin wani abu wanda ba dan Adam ba. Ya zama wajibi mu rungumi Fasahar (AI) domin itace duniyar kimiya da fasaha ta ke yayi kuma itace goben tsarin kimiya na duniya. A wannan rubutun zamu yi bayani daki daki akan fasahar (AI) da kuma yanda zata taimaka wajen inganta rayuwarmu ta ko wanne bangare. 

YANDA ZAMU INGANTA RAYUWARMU TA HANYAR AMFANI DA  FASAHAR ARTIFICIAL INTELLIGENCE (AI)



Tarihin Fasahar AI 

Tarihin kirkirarriyar fasahar AI ya samo asali ne tun a tsakiyar karni na 20 a shekarar 1956 a lokacin da aka gudanar da wani taron karawa juna sani Wanda ya gudana a kwalejin Darmouth ta kasar Amurka. Taron ya tattaunane akan hanyoyin da za ake bi wajen maganje matsalalolii ta hanyar amfani alamomi https://home.dartmouth.edu/about/artificial-intelligence-ai-coined-dartmouth. A karni na ashirin da daya (21st Century) fasahar AI ta samu fadada ta hanyoyi da dama irinsu yin tunani da magance matsalar da take da bukatar nazari, karantar dabi’u da halayen abun da ya mu’amalanceshi, kwaikwayo da kuma ajiye bayanan abun da ya mu’amalanceshi ko kuma aka umarceshi da yayi. 


RARRABE RARRABEN FASAHAR AI 

Fasahar AI ta rarrrabu kashi kashi dai dai da ake da buqata tayi. Wadannan sune mafi muhimmanci daga cikinsu

  • Machine Learning (ML): wannan yana daya daga cikin fasahar AI mafi karfi a duniyar kimiya da fasaha domin ta hanyar wannan fasahar akan iya koyawa wani abu ya karbi bayanai akan wani lamari sannan yayi harsashe akansa kuma ya fitar da mafitar da ta dace da wannan lamarin batare da wata tangarda ba. 

  • Natural language processing: Ta hanyar wannan fasahar na’ura ta kan iya fahimtar yaren da dan Adam yake yi mata magana dashi, ta fassara yaren kuma ta iya mayar dashi wani yaren na daban. Misali fasahar fassara, fasahar chart bort (Chart GPT) da dai sauransu

  • Computer Vision: A wannan bangaren za a iya koyawa na’ura ko kuma abu makamancin haka yanda zaike iya gane abu ta hanyar fahimtar abun wato ya fahimci siffar wani abu sannan ya iya tantace shi, misali fasahar bude waya da hoton fuska . 

  • Robotics: Robotics ko kuma muce Saqago da yaren Hausa wani tsarin kimiya ne wanda yake bayarda da dama a qirqiri wani abu wanda zai ke iya yin aiki na zahiri wanda dan Adam yakeyi kamar irinsu dakon kaya, yin tiyata a asibiti, aikin gadi da dai sauransu

  • Expert system: Wannan wani tsarin fasahar AI ne wanda zaike aiwatar da abu irin na kwararru, a wannan fasahar AI zai iya yanke hukunci da ya shafi kamfani, ma’aikata ko kuma akan wani wani lamari mai matukar muhimmanci  kamar yanda dan Adam zai iya yankewa 

A KARSHE

Daga bayanan da muka samu game da rarrabe rarraben AI zamu gane cewa fasahar AI zata shafi dukkan wani bangare na rayuwar dan Adam kuma tazo ne ta saukakawa dan Adam aikinsa na yau da kullum. A wannan zamani zabi biyu ne damu: mu rungumi fasahar AI sai mu tsira da ayyukanmu ko kuma mu gujeshi mu koma yan zaman kashe wando. 

Ku biyomu domin samun cikakkun bayanai akan kirkirarriyar fasahar (AI) da kuma hanyoyin da zamu bi muyi amfani da ita. 


#abokinaAI #AI